Hukumar lafiya ta duniya ta ce akalla yara miliyan daya sun samu allurar rigakafin cutar zazzabin cizon sauro zagayen farko a nahiyyar Afirka

0 60

Hukumar lafiya ta duniya WHO ta ce akalla yara miliyan daya a Afirka sun samu allurai daya ko fiye da haka na rigakafin cutar zazzabin cizon sauro zagayen farko a nahiyyar.

Hukumar ta kuma ce, an sanya kananan yara a Ghana, Kenya, da Malawi cikin wani sabon shirin yakar cutar.

Gigakafin cutar zazzabin cizon sauro, wanda gwamnatin Malawi ce ta fara kaddamar da shi a watan Afrilun 2019, ya nuna cewa maganin yana da lafiya kuma yana iya rage kaifin cizon sauro.

Har ila yau, ta ce, idan aka baza rigakfin a ko’ina, hukumar ta yi kiyasin cewa, allurar rigakafin za ta iya ceton rayukan wasu kananan yara ‘yan Afirka dubu 40 zuwa dubu 80 a kowace shekara.

Leave a Reply

%d bloggers like this: