Labarai

An bayyana bashin da ake bin jihar Jigawa na naira miliyan dubu 42 da miliyan 700 a matsayin daya daga cikin mafiya karanci a Najeriya

An bayyana bashin da ake bin jihar Jigawa na naira miliyan dubu 42 da miliyan 700 a matsayin daya daga cikin mafiya karanci a kasarnan.

Kwamishinan kudi da tsara tattalin arziki, Babagana Umar Gantsa, shine ya sanar da haka yayin wata ganawa da manema labarai.

Yace alkaluman dorewar basuka na 2021 wanda alkaluman hukumar kula da basuka suka tabbatar, jumillar basukan da ake bin Jigawa a kasashen waje ya kama naira miliyan dubu 11 da miliyan 800, yayin da basukan da ake bin jihar a cikin kasa ya tsaya a naira miliyan dubu 30 da miliyan 900.

Kwamishinan yace kididdigar bashin idan aka kwatanta da kudaden shiga wanda ma’aikatar kudi ta tarayya ta lissafawa jihar Jigawa a shekarar 2021 yana kan naira 7 da kwabo 53, yayin da idan aka kwatanta da ma’aunin GDP kuwa, yana akan kashi 4.14 cikin 100.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: