Sojojin Najeriya a jiya da yamma, sun dakile wani hari da aka kai wa al’ummar Malari, a karamar hukumar Mafa.

An kai harin ne a asibitin ‘yan sanda na Alkomi, daura da garejin Muna, dake kan titin Dikwa a birnin Maiduguri na jihar Borno da misalin karfe 7:00 na dare.

Kamfanin Dillancin Labarai na kasa NAN, ya samu labarin cewa an ji karar fashewar wasu kararrakin kayan fashewa, sai kuma karar harbe-harbe da aka yi na tsawon mintuna 30.

A cewar wata majiya, maharan da ake zargin ‘yan kungiyar Boko Haram ne, sun kaddamar da harin ne a kan rundunar sojojin da ke gadin ramuka a yankin.

Mutane da yawa, ciki har da mata da yara, sun yi tururuwa zuwa Cibiyar tsaro ta birnin.

An hangi mata da yara suna garzaya zuwa yankunan dake jihar Yobe.

Amma har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar Borno ba ta mayar da martani kan lamarin ba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: