Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta umarci da gudanar da bincike kan jami’in da aka gani yana kada kuri’a a yayin babban taron jam’iyyar APC na Kano

0 77

Rundunar ‘yan sanda ta kasa ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan jami’in da aka gani yana kada kuri’a a yayin babban taron jam’iyyar APC na ranar Asabar a jihar Kano.

A hoton bidiyon, an ga jami’in a kusa da Abdullahi Abbas, sabon zababben Shugaban jam’iyyar bangaren Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.

A cikin wata sanarwa, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda mai kula da shiyya ta daya a Kano, Abubakar Zayyanu, ya ce Mataimakin Sufeto Janar, mai kula da shiyyar, Abubakar Sadiq Bello, ya bayar da umarnin binciken jami’in.

A cewar sanarwar, Mataimakin Babban Sufeton ya bayyana lamarin a matsayin wanda bai dace ba.

An bayar da rahoton cewa jami’in dan sandan da aka bayyana sunansa da Bashir Mohammed yana aiki a gidan gwamnatin Kano, daga nan aka tura shi aiki tare da shugaban jam’iyyar APC na jihar.

Mataimakin Sufeto Janar din ya tabbatar wa jama’a cewa za a sanar da cigaban da aka samu dangane da lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: