Gwamnatin jihar Bayelsa ta sanya dokar hana zirga-zirga daga magariba zuwa wayewar gari akan hanyoyin ruwan ta

0 84

A wani mataki na dakile fashin teku, garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka, gwamnatin jihar Bayelsa ta sanya dokar hana zirga-zirga daga magariba zuwa wayewar gari akan hanyoyin ruwan ta.

Gwamnan jihar Duoye Diri ya sanar da matakin a jiya da yamma, a karshen taron majalisar tsaro na jihar karo na 12, wanda aka yi a gidan gwamnati dake Yenagoa, babban birnin jihar.

Gwamnan ya kara da cewa dokar hana zirga-zirgar ruwa, wacce za ta fara aiki nan take, tana tsakanin karfe 7 na maghriba zuwa 6 na safe, kamar yadda ya kuma sanar da hana amfani da jiragen ruwa masu gudu sosai.

Da yake yiwa manema labarai karin haske kan sakamakon taron, mai bayar da shawara na musamman kan harkokin tsaro, ya ce daga yanzu, ba za a bayar da izinin amfani da jiragen ruwa masu gudu sosai ba, yana mai gargadin cewa masu karya dokar za su fuskanci fushin hukuma.

Sai dai, yace za a sami rangwamen dokar yayin bukatar gaggawa, a lokutan dokar hana zigar-zirgar, inda yayi kira ga mutanen Bayelsa da su kai rahoton masu take dokar ga jami’an tsaro na jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: