Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta gargadi matasa da su guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jihar

0 77

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta gargadi matasa da su guji duk wani abu da zai kawo cikas ga zaman lafiya da ake samu a jiharnan.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, Lawan Shiisu Adam ya fitar, ya ce gargadin ya zama wajibi biyo bayan tashin hankalin da wasu fusatattun matasa ke haddasawa a wasu jihohin.

Ya kuma yi kira ga matasa da kada su bari mutane marasa daraja a cikin al’umma su yi amfani da su wajen tayar da zaune tsaye domin kawar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jiharnan.

Lawan Shiisu ya ce babu wanda ke da hurumin hukunta wanda ake tuhuma ta daukar doka a hannu sai dai a mika shi ga ‘yan sanda ko wasu jami’an tsaro domin daukar matakin da ya dace.

Ya kuma yi kira ga kungiyoyin addini, sarakunan gargajiya, kungiyoyin dalibai, kungiyoyin fararen hula, kungiyoyin mata da iyaye akan bukatar wanzar da zaman lafiya da mutunta juna.

Leave a Reply

%d bloggers like this: