Labarai

Hukumar EFCC ta sake gurfanar da Sambo Dasuki da tsohon gwamna Attahiru Bafarawa da tsohon ministan kudi Bashir Yaguda da wasu mutane biyu bisa zargin karkatar da kudi naira miliyan dubu 23 da miliyan 300

Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a jiya ta sake gurfanar da Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, da tsohon gwamna Attahiru Bafarawa, da tsohon ministan kudi, Bashir Yaguda, da wasu mutane biyu, bisa zargin karkatar da kudi naira miliyan dubu 23 da miliyan 300.

Sauran wadanda aka gurfanar sun hada da dan Attahiru Bafarawa, Sagir Bafarawa, da kamfanin su na Dalhatu Investment.

An gurfanar da su ne a kan tuhume-tuhume 25 dake da alaka da sama da fadi da kuma karbar kudaden haram.

An fara gurfanar da wadanda ake tuhumar ne a shekarar 2015 a gaban mai shari’a Peter Afen wanda a yanzu ya zama alkalin kotun daukaka kara.

Daga baya an sake gurfanar da su a gaban mai shari’a Husseini Baba Yusuf, wanda yanzu shi ne babban alkalin babban birnin tarayya Abuja, kafin daga bisani a gaban mai shari’a Yusuf Halilu.

Hukumar EFCC ta zarge su da karkatar da kudade daga ofishin mai bawa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro tsakanin shekarar 2013 zuwa 2015 domin gudanar da yakin neman zabe.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: