Rundunar Yan Sandan Jihar Zamfara sun tabbatar da cewa yan Bindiga sun sace Matasa Masu Yiwa Kasa Hidima 2 wanda suke kan hanyar su ta zuwa Jihohin Kebbi da Sokoto.

Kakakin Rundunar Yan Sandan Jihar Mohammad Shehu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a birnin Gusau.

Mohammad Shehu, ya ce rundunar ta samu rahoton sa ce masu yiwa kasa hidima su 2 daga wurin Shugaban Hukumar na Jihar Zamfara.

Kakakin Rundunar ya ce Matasa sun fito ne daga Benue da nufin zuwa Jihohin Kebbi da kuma Sokoto, kuma an sace Matasan ne a kan hanyar Tsafe zuwa Gusau.

Haka kuma kakakin rundunar ya ce Kwamishinan yan sandan Jihar Mista Ayuba Elkanah, ya samu labarin sa ce Matasan ne a lokacin da ya ziyarci Sansanin Horas da Matasan a karamar hukumar Tsafe ta Jihar.

Kazalika, ya ce Kwamishinan ya tura rundunar ta musamman domin kubutar da matasan akan lokaci. 

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: