Sabbin kwamishinonin hukumar zabe ta kasa (INEC) guda biyu da shugaba Buhari ya rantsar

0 63

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin hukumar zabe ta kasa (INEC) guda biyu a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Sabbin kwamishinonin sun hada da Muhammad Kallah daga jihar Katsina da Kunle Ajayi daga jihar Ekiti.

Majalisar dattawa ta tabbatar da su a watan Yulin bana.

Wata sanarwa da ofishin mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar ta ce, shugaban kasar ya kaddamar da Kallah da Ajayi kafin kaddamar da eNaira da kuma tambarin ranar tunawa da sojojin kasarnan ta bana.

Ya ce tun a ranar 15 ga watan Satumba shugaba Buhari ya rantsar da uku daga cikin kwamishinonin hukumar da aka tabbatar.

Wadanda aka rantsar a lokacin sun hada da Baba Bila mai wakiltar shiyyar arewa maso gabas da Sani Adam mai wakiltar arewa ta tsakiya da Abdullahi Abdu mai wakiltar arewa maso yamma.

Leave a Reply

%d bloggers like this: