Sabbin Naɗanaɗen Buhari An Rufe Kura Da Fatar Akuya

0 226

Shugaba Muhammadu Buhari ya sake naɗa Injiniya Boss Mustapha a matsayin Sakataren Gwamnatin Tarayya, SGF da Abba Kyari a matsayin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, CoS.

Garba Shehu, mai magana da yawun Shugaban Ƙasa ya bayyana haka a shafinsa na Twitter ranar Juma’ar nan.A cewar Mista Shehu, dukkan naɗe-naɗen sun fara aiki ne tun ranar 29 ga Mayu, 2019.

Haka kuma, Shugaban ya naɗa wasu mataimakansa na musamman har 11 da suka haɗa da:

Mohammed Sarki Abba –Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa Kan Harkokin Gida da TarukaYa’u Shehu Darazo – Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban (Ayyuka na Musamman) Dokta Suhayb Sanusi Rafindadi – Likitan Shugaban Ƙasa

Ambasada Lawal A. Kazaure – Babban Jami’in Tsare-tsare na Fadar Shugaban ƘasaSabiu Yusuf – Mataimaki na Musamman (Ofishin Shugaban Ƙasa)Saley Yuguda – Mataimaki na Musamman (Kula da Gida)Ahmed Muhammed Mayo – Mataimaki na Musamman (Kuɗaɗe da Gudanarwa)Mohammed Hamisu Sani –Mataimaki na Musamman (Ayyuka na Musamman)Friday Bethel – Mataimaki na Musamman (General Duties)Sunday Aghaeze – Mataimaki na Musamman(Mai Ɗaukar Hoto na Fadar Gwamnati)Bayo Omoboriowo Mataimaki na Musamman (Mai Ɗaukar Hoton Shugaban Ƙasa).

Tun bayan fitowar waɗannan sunaye ne dai mutane ke ta cigaba da bayyana raayinsu, yayin da wasu ke ganin tuwon jiya za a sake tukawa babu wani sauyi.

Yawancinsu sun yi aiki da Shugaban a wa’adin mulkinsa na farko.

Leave a Reply

%d bloggers like this: