Sama da Mutane 140 ne Suka Kamu da Cutar Sankarau a Jigawa.

0 95

Ma’aikatar lafiya a jihar jigawa ta tabbatar da samun mutane 141 wadanda suka kamu da cutar sankarau yayinda cutar tayi ajalin mutane 8 a jihar.

Babban sakatare a ma’akatar lafiya Dr Salisu Mu’azu shine ya tabbatar da samun cutar ga wakilin mu Zulkiflu Abdallah Dagu a Dutse. Babban sakaratan wanda yayi magana hanyar Dr Sabi’u Muhammad yace an samu cutar a wasu yan kuna na karamar hukumar Kaugama,Birniwa da kuma karamar hukmar Maigatari.

Dr Muhammad yace akwai mutane 134 daga cikin 141 wadanda suka harbu da cutar samfurin C,yayinda aka samu mutum guda dauke da cutar samfurin X,yayinda cutar tayi sanadiyyar mutuwar mutane 8.

Yace yanzu haka ana daukan dukkan matakan da suka dace domin yaki da cutar a yankunan da ta barke,sanna kuma an shawarci mazauna yankunan da suna sanya ido sosai tare da kai wanda ya harbu da cutar zuwa ga babban asibiti mafi kusa domin gwamnati ta samar da magani kyauta ga masu da cutar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: