Sama da ‘yan ƙasar Habasha millyan huɗu ne suke gararamba a sassa daban-daban na ƙasar

0 718

Hukumar kula da ƙaurar jama’a ta Majalisar Dinki Duniya ta ce sama da ‘yan ƙasar Habasha millyan huɗu ne suka rasa muhallansu, inda suka gararamba a sassa daban-daban na ƙasar.

IOM ta ce mutanen sun tsinci kansu cikin annan hali ne sakamakon yawaitar tashe-tashen hankula da matsalar fari.

Wannan na kunshe cikin rahoton da hukumar ta fitar, wanda aka yi nazari daga watan Nuwambar 2022, zuwa Yunin 2023.

Rahoton ya ce kashi biyu cikin uku na mutanen tashin hankalin da ya ɓarke tsakanin sojojin ƙasar da ‘yan tawayen Tigray ne ya tilasta musu barin gidajensu.

Wanna ne karon farko da wani rahoto ya yi cikakken bayani kan yadda yakin ya daidaita Tigray, wanda yanki ne daga cikin inda ake cike da al’uma a Habasha. Yankin Somaliya da ke gabashin ƙasar dama can na fama da matsalar fari, inda MDD ta yi kiyasin kusan ‘yan Habasha miliyan 20 ne ke tsananin bukatar taimakon abinci mai gina jiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: