Sanatoci: wa za a dorawa alhakin karuwar rashin tsaro a fadin kasarnan, PDP ko APC?

0 114

Sanatoci sun yi musayar yawu a tsagin jam’iyyu a jiya kan wanda za a dorawa alhakin karuwar rashin tsaro a fadin kasarnan.

Yayin da sanatocin jam’iyyar PDP suka yi Allah-wadai da shirun da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi dangane da sace-sacen mutane da kashe-kashen da ake yi a fadin kasarnan, su kuma ‘yan jam’iyyar APC mai mulki basu yarda da hakan ba, suna masu cewa gwamnatin Buhari na iyakar kokarinta wajen magance rashin tsaro.

Gungun marasa rinjaye na jam’iyyar PDP a majalisar kasa ne ya fara bayyana matsayinsa. ‘Yan majalisar, karkashin jagorancin Shugaban Marasa Rinjaye na Majalisar Dattawa, Enyinnaya Abaribe, sun zargi Buhari da cewa ba wai karya kundin tsarin mulki ba kadai, har ma da rashin zuwa aiki a yayin da ake fuskantar tsananin rashin tsaro a kasarnan.

A martaninta, gungun sanatocin jam’iyyar APC ya ce ‘yan PDP a majalisa sun wuce gona da iri idan aka yi la’akari da kyakkyawar alakar aiki dake akwai a majalisar.

Da suke magana da manema labarai a jiya, gungun ‘yan APC karkashin jagorancin shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawa, Abdullahi Yahaya, ta bayyana kalaman na Abaribe da cewa za su iya dumama yanayin da tuni yake cikin zafi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: