Gwamna Badaru ya jaddada janye dokar hana gudanar da hawan dawakai a Jigawa

0 115

Gwamnan Jihar Jigawa Muhammad Badaru Abubakar ya janye dokar hana gudanar da hawan dawakai da sauran bukukuwa a lokacin Sallah karama a jiharnan.

Gwamnan ya sanar da haka a jiya lokacin da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan zaman ganawa kan tsaro da aka gudanar a dakin taro na Ahmadu Bello dake Dutse.

Yayi bayanin cewa janye dokar hana hawan dawakan da sauran bukukuwan Sallah ya biyo bayan nasarorin da aka samu a yaki da cutar corona a jiharnan.

Gwamnatin jihar Jigawa a bara ta soke bukukuwan Sallah ciki har da hawan dawakai domin rage bazuwar cutar corona.

Gwamnan yayi bayanin cewa halin da ake ciki dangane da corona a kasarnan a bara, shi ya tursasa soke hawan dawakan.

Gwamna Badaru yace za a gudanar da hawan dawakai da sauran bukukuwan Sallah a bana bisa kiyayewa da dokokin kariya daga corona.

Leave a Reply

%d bloggers like this: