Tsohon shugaban Majalisar Datatwan Najeriya Dr Bukola Saraki ya roki ‘Yan kasar da su sake baiwa Jam’iyyar PDP damar sake jagorancin Najeriya a shekarar 2023 domin fitar da ita daga cikin  dimbin matsalolin da suka addabe ta.

Saraki yace Najeriya ayau na cikin mawuyacin hali sakamakon tabarbarewar tsaro da matsalar tattalin arziki wanda Jam’iyyar su ta PDP ke iya kawo sauyin da zasu magance su.

Tsohon shugaban Majalisar yace kasar na fuskantar wani yanayi mai matukar wahala, yayin da ya sha alwashin ganin sauyi muddin Yan Najeriya suka baiwa Jam’iyyar su ta PDP damar sake jagorancin ta.

Dr Bukola Saraki dake jagorancin kwamitin sasanta ‘yayan Jam’iyyar PDP da zummar warware matsalolin da suka biyo bayan zaben shekarar 2019 yace sun koyi darasi dangane da irin matsalolin da suka fuskanta a baya, kuma yanzu haka sun shirya jagorancin kasar wajen dora ta kan tafarkin cigaba.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: