Sarkin Dutse Ya Karbi Bakuncin Kwamandan Runduna Ta 26 Masu Sulke

0 102

Mai Martaba Sarkin Dutse, Alhaji Hamim Nuhu Sanusi ya karbi bakuncin kwamandan runduna ta 26 masu sulke Birgediya Janar Haruna Muhammad Abubakar.
Sarkin a lokacin da yake karbar kwamandan da tawagarsa a fadarsa, ya yaba da kafa runduna ta 26 ta sulke a Dutse.
Ya kuma yi alkawarin tallafawa sojojin Najeriya domin samun nasara a jihar.
Hamim, ya bayyana jin dadinsa na samun kafa rundunar soji a Masarautar sa.
Da yake jawabi yayin ziyarar, kwamandan ya yabawa Sarkin da ‘yan majalisarsa bisa kyakkyawar tarbar da suka yi masa da mukarrabansa.
Ya bayyana cewa, rundunar 26 na daga cikin sabbin Brigade da aka kafa a rundunar sojin Najeriya domin dakile kwararar masu aikata laifuka acikin kasarnan.
Ya kara da cewa ya kai ziyarar ne domin hadin gwiwa da masarautun gargajiya wajen samun nasarar gudanar aiyukansu jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: