‘Yan Bindiga Sun Sace Akalla Mutane 100 A Gonaki A Jihohin Zamfara da Katsina.

0 80

‘Yan bindiga sun sace akalla mutane 100 a gonaki a jihohin Zamfara da Katsina.
Manema lanarai sun tattaro cewa ‘yan bindiga dauke da makamai sun kai hari a garin Wanzamai da ke kan iyakar Zamfara da Katsina.
Al’ummar da ke kan hanyar Gusau da Funtua, sun sha fama da hare-haren ‘yan bindiga a baya.
Wani mazaunin kauyen Wanzamai da ke karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara mai suna Sani Wanzamai ya ce an yi garkuwa da yara kusan 80 daga kauyen Wanzamai tare da wasu fiye da 20 daga kauyen Kucheri da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar da kuma al’ummar Yankara ne a makwabciyar Katsina.
Yayin da yaran suka shiga daji su debo itace, sauran manya kuma an yi garkuwa da su ne a filayen noma a lokacin da suka je aikin noman gona a shirye-shiryen noman bana. Akwai kuma mata a cikin wadanda abin ya shafa
Masu garkuwar basu tuntubi wani dangi ba tukuna. Wasu iyalai sun yi ƙoƙari neman mutanen da abin ya shafa amma ba su samu ko ɗaya ba.
Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, CSP Muhammad Shehu, mun kasa samun jin ta bakinsa har zuwa lokacin hada wannan rahoton saboda wayarsa a kashe take.

Leave a Reply

%d bloggers like this: