WHO Na Fuskantar Kalubale Wajen Magance Yawan Mace-macen Mata Masu Juna Biyu.

0 98

Hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce har yanzu magance matsalar mace-macen mata masu juna biyu a yawancin jihohin Arewa ta Tsakiyar kasarnan, ciki har da jihar Neja, na fuskantar kalubale ga kungiyar duk da kokarin da ake yi na rashin tsaro.
Kungiyar ta ce ba a yi wa yara da dama allurar riga-kafi a yankin ba saboda kalubalen tsaro da ake fama da shi a galibin jihohin yankin.
Ko’odinetar hukumar ta WHO a shiyyar Arewa ta Tsakiya, Dakta Asma’i Zeenat Kabir, ta bayyana haka a wajen taron tunawa da ranar lafiya ta duniya na shekarar 2023 da kuma cika shekaru 75 da kafa kungiyar da aka gudanar a Minna babban birnin jihar Neja.
Zeenat ta ce an samu ci gaba da dama a cikin shekaru 70 da suka gabata ta fuskar kare mutane daga cututtuka masu kisa da suka hada da kawar cutar sankarau, yayin da aka ceto rayukan miliyoyin yara ta hanyar rigakafin yara, tare da raguwar mace-macen mata masu juna biyu, da sauransu.
Tun da farko, kwamishinan lafiya na jihar Neja, Dr Mohammed Mohammed Makusidi, ya ce gwamnatin jihar Neja ta samu ci gaba a fannin kiwon lafiya a matakin farko a cikin shekaru takwas da suka gabata ta hanyar gina karin ingantattun cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin tabbatar da kiwon lafiya a fadin jihar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: