Sarkin Musulmi Ya Bukaci Yan Najeriya Su Yiwa Kasar Addu’a A Kwanaki Goman Karshen Ramadan

0 79

Kungiyar Jama’atu Nasril Islam karkashin mai alfarma sarkin musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, ya bukaci al’umar musulmi da suyi amfani kwanaki 10n karshe na watan azumin ramadan wajen sanya Najeriya cikin Adduoin zaman lafiya, da cigaba da bunkasar tattalin arziki.

A cikin wata sanarwa da babban sakatare na kungiyar Dr Khalid Abubakar Aliyu ya fitar ya bukaci yan najeriya musulmi dake gida da kuma wanda ke gudanar da ibadar Umara a kasa mai tsarki da su gudanar da Adduoi ga gwamnati mai jiran gado.

Sanarwar ta kuma tinatar da yan najeriya muhimmancin kwanaki 10 na karshen watan ramadana tare kebabben dare mai alfarma, wanda yafi watanni dubu alheri kamar yadda addinin musulunci ya koyar.

Haka kuma kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta bukaci al’umar musulmi da su mayar da hankali wajen mihimmancin lokacin da dumbin ladan ake samu, wajen neman gafara da kuma karatun al’kurani mai tsarki, halastar darussan karatuttukan tafsirai da kuma taimakon mabukata da kame baki wajen furta kalamai da zasu jawo fushin Allah.

Leave a Reply

%d bloggers like this: