Gwamnatin Bauchi Zata Dauki Mataki Kan Duk Masu Wa’azin Da Aka Samu Da Kawo Rudani A Jihar

0 67

Gwamnatin jihar Bauchi zata dauki mataki kan duk masu wa’azi da aka samu da amfani da kalamai wajen kawo rudani a jihar.

Sakataren gwamnatin jihar Ibrahim Kashim yayi gargadin bayan wani taron gaggawa da hakumomin tsaro suka gudanar a gidan gwamnatin jihar.

Ibrahim Kashim ya bayyana rashin jin dadin sa kan salon da wasu masu wa’azi a jihar ke amfani dashi wajen tayar da zaune tsaye da raba kan al’uma, inda yace gwamnatin jihar zata dauki mataki kan dun wanda aka samu.

A cewar sa duk abinda ya shafi addini lamari ne mai sarkakiya da ba kowa ya kamata ya tsoma baki ba, musamman kan matsaalolin da masu ilimi da dalibai ne kawai zasu iya fuskanta.

Gwamnatin jihar ta kuma umarci hakumonin tsaro dasu tarwatsa kungiyar Sara Suka dake addabar mutane musamman a cikin kwaryar birnin Bauchi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: