Shan matsin lamba ya tilasta wa Gwamna El-Rufai fasa karbar kudi shiga filin Sallar Idi a jihar Kaduna

0 53

Gwamnatin Jihar Kaduna da ke arewacin Najeriya ta janye matakinta na karbar harajin N500, 000 kafin ta bayar da izinin amfani da wani babban fili da ke birnin Kaduna domin gudanar da Sallar Idi.

Gwamnatin ta fasa karbar haraji domin bai wa wasu Musulmai damar yin amfani da filin Murtala Square wajen gudanar da Sallah Idi bayan ta fuskanci matsin lamba.

Batun ya tayar da jijiyoyin wuya bayan da ‘yan kwamitin masallacin Kano Road, wadanda ke amfani da filin wajen gudanar da sallar a duk shekara, sun bayyana mamakinsu kan matakin ganin cewa sun kwashe shekara da shekaru suna sallar Idi a cikinsa ba tare da bayar da ko sisi ba.

Daya daga cikin mambobin kwamitin, Malam Sabi’u Garba, ya shaida wa BBC cewa ba su ji dadin harajin da gwamnati ta sanya musu na amfani da filin ba.

“Wannan wani abu da da ba mu taba jin sa ba, a ce mutum zai yi sallah sai ka biya kudin ibadar da za ka yi a arewacin Najeriya. Wannan wuri da muke sallah, Sardauna ma a nan ya rika sallah…iyayenmu da kakaninmu sun tabbatar da cewa an ba su takardun izinin (amfani da wurin don yin sallar Idi),” in ji shi.

Sai dai jim kadan bayan wadannan kalamai gwamnatin Jihar ta Kaduna ta janye matakin nata.

Mista Anthony Richard, mai magana da yawun kwamitin kula da kasuwanni na Jihar ya gaya wa BBC cewa tun da farko sun dauki matakin karbar harajin ne saboda an yi gyare-gyare a filin don haka ba za a bar ‘yan siyasa da masu gudanar da sha’anin addini su yi amfani da shi ba sai sun biya haraji. Amma ya ce sun fasa karbar kudin yana mai cewa ba matsin lamba ba ne ya sa aka janye aniyar.

“Akwai tsarin da aka fitar domin kokarin ganin cewa ba a rika ayyuka na addini ko na siyasa. An canza tsarin Murtala Square ne baki daya, yadda yake yanzu ya bambanta da yadda yake a baya,” a cewar Mista Richard.

Leave a Reply

%d bloggers like this: