Sharuɗɗan belin Dakta Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi

0 389

Sharuɗɗan belin da aka ba fitaccen malamin addinin musuluncin nan na jihar Bauchi kuma babban limamin masallacin Juma’a na Dutsen Tanshi, Dakta Idris Abdulaziz, ya hana a sake shi daga gidan yari.

A ranar Laraba ne dai kotun ta ci gaba da zaman shari’ar malamin dake tsare a gidan yari kwanaki 30 bisa samunsa da laifin cin mutuncin kotu.

Lauyan wanda ake kara, Abubakar Sadiq, ya gabatar da cewa kotun ba ta da hurumin ci gaba da shari’ar biyo bayan umarnin da babbar kotun tarayya ta 7 da ke Bauchi ta bayar wanda ya umurci Kotun Shari’ar Musulunci da ta dakatar da shari’ar tare da mika mata bayanan karar.

Bayan tattaunawa kan batutuwan da suka shafi bayar da belin limamin da bangarorin biyu suka yi, Alkalin Kotun Shari’ar Musulunci ta 1, Malam Hussaini Turaki, ya bayar da belinsa tare da mutane uku, Hakimin gundumar, da mai shaidar digiri na uku, Da kuma fitaccen dan kasuwa a cikin garin Bauchi.

Sawaba radio ta ruwaito cewa an fara tsare Abdulaziz ne a ranar 15 ga watan Mayun 2023 a gidan yari bisa zarginsa da tayar da hankalin jama’a da wata kotun majistare da ke Bauchi ta yi, bayan kwamishinan ‘yan sandan jihar Bauchi Alhassan Aminu ya gurfanar da shi a gaban kuliya.

Shehin malamin ya shafe kwanaki bakwai a gidan yari duk da cewa an bayar da belinsa a kan kudi Naira miliyan daya da kuma wasu mutane uku da suka tsaya masa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: