Shekara guda kenan da ayyana Corona a matsayin annoba

0 150

Kungiyar masu alkinta mahalli ta kasa da kasa a rahotanta da ta fitar a wata mujalla ya ce annobar Corona ta hana alkinta muhalli banda illar da ta yi wa tattalin arziki da bil adama.

Bullar cutar Coronavirus a duniya, ba kawai tattalin arziki da bil adama ba ne ta yi wa illa, hatta yunkurin alkinta mahalli ma  ba a bar shi a baya ba, in ji wani rahoto da kungiyar alkinta mahalli ta kasa da kasa ta fitar a wata mujalla.

Bayanan hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake cika shekara guda cur da ayyana cutar a matsayin annoba.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ce ta ayyana cutar ta Corona a matsayin annoba a shekarar bara ta 2020, bayan da aka fara samun bullarta a birnin Wuhan na kasar Sin.

Sai dai wani bincike da masana suka yi a ‘yan makwannin da suka gabata, sakamakon farko-farko na nuni da cewa ba a Wuhan ba ne cutar ta samo asali.

Leave a Reply

%d bloggers like this: