Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta bayar da umarnin cigaba da amfani da allurar rigakafin Kamfanin AstraZeneca bayan da wasu kasashe suka kaurace mata.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya WHO ta ce babu wani dalilin dakatar da amfani da alluran rigakafin Corona ta Kamfanin AstraZeneca. Mai magana da yawun hukumar Margaret Harris ta shaidawa manema labarai a birnin Geneva cewa, kwamitin kwararru na hukumar sun tabbatar da inganci rigakafin kana kuma ta wannan hanyar ce za a samu saukin cutar.

A baya bayan nan dai kasashen Denmark da Norway da Iceland sun dakatar da aiki da allurar, inda su kuma kasashen Italiya da Ostraliya suka haramta amfani da ita kwata-kwata a kasashensu, bisa dalillan da suka bayar na cewa allurar ta haddasawa wadanda aka yi wa ita dunkulewar jini. Annobar ta COVID-19 ta yi ajalin mutane sama da miliyan biyu a fadin duniya, yayin da wasu miliyoyi ke can kwance a asibiti.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: