Majalisar Tarayya ta bukaci Rundunar Sojin Najeriya ta bi mayakan Boko Haram har maboyarsu ta ragargaje su.

Majalisar Wakilia ta yi kiran ne tana kuma mai neman Gwamnatin Tarayya ta sauya salon yakinta ta kuma magance hare-haren Boko Haram da ake samu a Maiduguri, Jihar Borno.

Ta yi kiran ne bayan kudurin da Honorabul Abdulkadir Rahis ya gabatar inda yake korafi kan yawitar hare-haren kungiyar a baya-bayan a Maiduguri.

Zauren Majalisar Wakilan ya kuma yi kira ga Ma’aiakatar Agaji a Ayyukan Jinkai da Hukumar Agajin Gaggawa ta Ksa da su hanzarta samar da kayan tallafi ga mutanen da hare-haren suka shafa.

A baya-bayan nan an samu hare-haren kungiyar Boko Haram a kewayen garin Maiduguri, amma sojoji sun fatattaki mayakan.

A kwanakin baya, mayakan sun kai wa sojoji hari a garuruwar Marte da Dikwa, har suka kora sojoji, kafin daga baya sojojin su fatattake su.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: