Shugaba Buhari Ya Gana Da Shugaban Gwamnatin Chadi Janar Mahamat Idriss Deby-Itno A Saudiyya

0 75

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da shugaban gwamnatin Chadi, Janar Mahamat Idriss Deby-Itno, sun gana jiya a Makkah, kasar Saudiyya, domin tattaunawa akan rikicin da ke wakana a kasar Sudan.

Da yake magana yayin wata ziyara da Deby-Itno ya kawo masa, Shugaba Buhari yace fadan da ake yi, wanda ya barke a babban birnin kasar Sudan tsakanin sojoji da mayakan kungiyar RSF, ba abin maraba bane.

Ya kuma bayyana fadan wanda ya jawo rasuwar gomman mutane da abin takaici.

Shugabannin biyu, a cewar wata sanarwa da kakakin shugaba Buhari, Garba Shehu ya fitar, sun bibiyi halin damuwar da ake ciki tare da yin kira ga dukkanin kasashen makota da sauran kasashen duniya da su sanya baki tare da shawo kan bangarorin biyu su dena fada tare da kulla yarjejeniya.

Shugaba Buhari ya yabawa Deby Itno bisa kokarinsa na ganin an samu zaman lafiya da lumana. Deby Itno ya bayyana halin da ake ciki a Sudan da abin tsoro, inda yace idan ba a kawo karshensa ba, zai shafi sauran kasashe makota.

Leave a Reply

%d bloggers like this: