Shugaba Buhari Ya Gana Da Wasu Gwamnoni Da Jami’an Gwamnati Domin Jin Bahasin Zaben Da Aka Kammala A Najeriya

0 73

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a jiya ya gana da wasu daga cikin gwamnoni da sauran jami’an gwamnati wadanda suka bashi bahasi akan halin da ake ciki, ciki har da kammala zabukan da suka rage a nan Najeriya.

Ya gana da su a fadar saukar baki ta Makkah, inda gwamnatin Saudiyya ta sauke shi.

Ya magantu a rana ta 5 ta ziyarar aikin da ya kai Saudiyya inda suka samu zaman fira cikin annushuwa.

Daga cikin wadanda Shugaba Buhari ya karbi bakuncinsu sune Gwamna Mai Mala na jihar Yobe da Babagana Zulum na jihar Borno da kuma gwamnan jihar Katsina mai jiran gado, Dikko Umar Radda.

Sauran, kamar yadda yazo a sanarwar da kakakinsa Garba Shehu ya fitar, sun hada da shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa da shugabar hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa, da tsohon babban hafsan sojin kasa, Janar Tukur Buratai mai ritaya. Shugaba Buhari yace dukkan nasarorin da Najeriya ta samu na alaka da karfin mulkinta na demokradiyya da hukumominta, wadanda a cewarsa, dole ne a karfafa su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: