Gwamnatin Tarayya Ta Saki 45.3Bn Domin Fara Aiwatar Da Shirin Farfado Da Tattalin Arzikin Da Cutar Corona Ta Daidaita.

0 164

Gwamnatin Tarayya ta amince da sakin kudi naira miliyan dubu 45 da miliyan 300 ga jihohi da babban birnin tarayya domin fara aiwatar da shirin farfado da tattalin arzikin da cutar corona ta daidaita.

Shugaban shirin na kasa, Abdulkarim Obaje, shine ya sanar da haka cikin wata sanarwa da ya fitar jiya ta hannun jami’in yada labarai na shirin, Suleiman Odapu.

Shirin, wanda na gwmanatin tarayya ne tare da hadin gwiwar bankin duniya, ana aiwatar da shi a jihohi 36 da babban birnin tarayya domin fadada tallafin rayuwa da samar da abinci da kudade ga talakawa da masu karamin karfi da kamfanoni.

Yace kudaden, wadanda aka raba a ranar Alhamis, anyi la’akari da sakamakon kowace jiha bayan auna kokarinta kamar yadda wani mai tantancewa mai zaman kansa ya tabbatar.

Yace sakamakon ya nuna cewa an samu cigaba sosai wajen cimma burin manufofin da shirin ya sanya a gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: