Shugaba Buhari ya isa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya

0 131

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, a yau Lahadi zai tafi birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron Zauren Majalisar Dinkin Duniya karo na 76th.

Tun a ranar Talata ne 14 ga watan Satumba aka fara taron a birnin New York.

Taken Taron na wannan Shekarar shine Farfadowa Daga Annobar Korona da Sake Gini Mai Dorewa da Girmama Haƙƙin Dan Adam da Kuma Yadda Za a Raya Majalisar Ɗinkin Duniya.

Kakakin Shugaban Kasa Malam Garba Shehu, shine ya bayyana hakan cikin wata sanarwa, inda ya ce shugaba Buhari zai yi jawabi ga Majalisar a ranar Juma’a.

Malam Garba Shehu, ya ce Shugaba Buhari zai yi jawabi kan taken taron, inda zai tattauna kan Lamuran da suka shafi Duniya.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai yi ganawar Diflomasiyya da sauran shugabannin kasashen Duniya da kuma hukumomin Cigaban kasashen Duniya.

Kazalika, sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai dawo gida Najeriya a ranar Lahadi 26 ga watan Satumba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: