Shugaba Buhari ya jaddada bukatar shugabannin kasashen Afirka da su hada karfi da karfe domin dakile ayyukan ta’addanci a nahiyar

0 74

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada bukatar shugabannin kasashen Afirka su hada karfi da karfe domin dakile ayyukan ta’addanci a nahiyar.

Ya bayyana hakan ne a jiya a wata sanarwa da mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, ya fitar domin jajantawa al’ummar kasa da shugaban kasar jamhuriyar Nijar Mohammed Bazoum kan kisan mutane 69 da ‘yan tawaye suka yi a kan iyakar kasar da Mali da Burkina Faso.

Shugaban kasar wanda ya bayyana matukar kaduwarsa da alhininsa kan lamarin, ya ce cin zarafi da ake yi wa mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, barazana ce a ko’ina a nahiyar Afirka, don haka akwai bukatar gaggawar kara hada kai a tsakanin kasashen Afirka wajen kawar da barazanar ta’addanci.

Ya kara da cewa wannan mummunan harin da aka kai kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba, ciki har da wani magajin gari a Jamhuriyar Nijar, wani koma baya ne ga kokarin da yankin ke yi na dakile ayyukan ta’addanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: