Shugaba Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Hako Danyen Mai Da Iskar Gas A Jihar Borno

0 70

A jiya ne shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar da aikin neman aikin hako danyen mai da iskar gas na Wadi-B a jihar Borno inda hakan ke nuna cewa an koma aikin hako danyen mai da iskar gas a yankin tafkin Chadi.

Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum, shi ne ya kaddamar da aikin a madadin shugaban kasar.

An fara aikin neman danyen man a shekarar 1995, yayin da aka sanar da gano man fetur a shekarar 2015 amma an dakatar da aikin saboda ‘yan tada kayar baya.

Shugaba Buhari ya ce tun daga lokacin ne kamfanin man fetur na kasa (NNPC) ya gudanar da bincike mai zurfi a dukkan iyakokin kasar, lamarin da ya kai ga samun nasarar ganowa tare da hako danyen mai da iskar gas masu yawa a kogin Kolmani na II a jihohin Bauchi da Gombe. Ya ce kamfanin na NNPC ya kuma bayar da haske kan aikin neman aikin hakar man fetur a jihar Nasarawa da kuma ayyukan sake fadada neman man a yankin tafkin Chadi wanda a cewarsa hakan zai inganta samar da makamashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: