Shugaba Buhari ya sake zargar yan kasuwa kan yadda farashin kayan abinci yake tashi a kasuwanni

0 100

Shugaban Kasa Muhammad Buhari ya sake zargar yan kasuwa kan yadda farashin kayan abinci yake tashi a kasuwanni.

Shugaba Buhari ya zargi yan kasuwar ne a lokacin da yake jawabi kan murnar cikar Najeriya shekaru 61 da samun yan cin kai daga turawan mulkin mallaka.

Shugaban Kasar ya ce yan kasuwa ne suka kirkiri tsadar kayan masarufin bayan sun boye kan abinci da nufin samun riba mai yawa.

Haka kuma ya ce fannin Noma na cigaba da taka muhimmiyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin kasar nan fiye da man fetur.

Muhammadu Buhari, ya koka kan cewa duk da irin tagomashin da fannin Noma yake samu, amma kuma Talakawa na cigaba da shan wahala, biyo bayan yadda wasu yan kasuwa suke boye kayayyakin Abinci domin a rika siyansa da Araha.

Kazalika, ya ce ya umarci Ma’aikatar Aikin Gona da Cigaban Karkara, ta farfado da hukumar Kula da Ajiyar Kayan Abinci tare da yin aiki da hukumomin tsaro, hukumar kula da hada-hadar sauyin kudade domin samarda mafita kan tsadar kayan masarufi.

A watan Yuli na shekarar 2021, shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya taba zargin yan kasuwa da boye kayan masarufi domin sayarwa da tsada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: