Shugaban Nijeriya  Muhammadu Buhari ya sanar da dakatar da zuwa mahaifarsa ta Daura domin ziyarar da ya saba zuwa a kowace sallar Idi. A cikin sanarwar da muka samu daga Garba Shehu da ke magana da yawun shugaban, Shugaba Buhari y ace ya shirya gudanar da Sallar Idi a Fadarsa da ke Abuja kamar yadda ya yi a shekarar da ta gabata saboda halin corona da duniya ke ci gaba da fuskanta.

Sanarwar ta ce Shugaba Buhari zai yi Sallar Idin da iyalensa da ma’aikatansa na kusa da shi da kuma wasu manyan ma’aikatan gwamnati. Sai dai shugabn ya ce da zarar an kammala sallar Idi ba zai karbi bakunci kowa ba kuma yana ba sauran jama’a shawara da a takaita haduwa a yayin bukukuwan sallar don dakile bazuwar annobar corona, yana mai cewa idan har za a yi shagulgulan a tabbata an bi dokokin kariya daga cutar ta COVID-19.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: