Rahotannin da Sawaba FM ke samu daga gidan talabijin na Aljazeera, na cewa a wannan Litinin ‘yan sandan Isra‘ila sun sake kutsa kai masallacin Al-Aqsa inda Musulmi Falasdinawa ke ibadar watan Ramadana. Yanzu haka sakamakon arangamar adadin mutane wadanda aka raunata sun kai 215.

A cikin su an kwantar da mutane 153 a asibiti ciki har da mutane 4 ke cikin matsanancin hali sakamakon munanan raunukan da suka ji.

Masallacin na Al-Aqsa dai na cikin masallatai guda uku masu tsarki a addinin Musulunci.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: