Yadda ake jimamin wadanda suka mutu a hadarin jirgin ruwa

0 262

Masu aikin ceto na ci gaba da laluben gawarwakin wadanda suka nutse a ruwa a sakamakon wani hadarin jirgin ruwa a jihar Nejan Najeriya a ranar Asabar da ta gabata.

Mutanen biyar na daga cikin wadanda suka nutse a ruwa bayan wani hadarin jirgin ruwa da ya yi sanadiyar rayukan mutum kimanin talatin a karshen mako, jirgin ruwan ya nutse da fasinjoji wadanda akasarinsu ‘yan kasuwa ne da ke kan hanyar komawa gidajensu da ke a Kauyen Tijana a yankin Munya a jihar ta Neja.

Wani mai magana da yawun Hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar, Ibrahim Audu Hussein, ya ce sun yi nasarar gano gawarwaki kimanin talatin kuma suna fadada bincike don gano sauran wadanda ba a gani ba, an dai yi nasarar ceto mutum sittin da biyar, da taimakon masuntan yankin inji Malam Husseini. 

A ranar Asabar din da ta gabata ne, hadarin ya auku bayan wata guguwar iska mai karfi da ta kada jirgin ruwan har ya daki wani katon dutse inda daga bisani jirgin ya kife, ana ganin ya dauko mutanen da suka wuce kima.

Leave a Reply

%d bloggers like this: