Shugaba Buhari ya taya murna ga gidan rediyo Najeriya dake Kaduna bisa cikarsa shekaru 60 da kafuwa

0 47

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga gidan rediyo Najeriya dake Kaduna, bisa cikarsa shekaru 60 da kafuwa.

Shugaban Kasar, cikin wata sanarwa daga kakakinsa, Femi Adesina, ya yabawa gidan rediyon bisa rawar da yake takawa wajen hada kan mutanen Najeriya tare da dawo da zaman lafiya da amincin juna a lokacin da bayan yakin basasa.

Shugaba Buhari cikin wani sakon bidiyo da aka nada da Hausa wanda ya aikawa shugabannin gidan rediyon domin murnar zagayowar ranar, ya jinjinawa gidan rediyon bisa shirye-shirye masu ilimintarwa, fadakarwa da nishadantarwa, wadanda ake yi domin masu sauraro daga ko’ina a Najeriya har da kasashe makota.

Shugaban Kasar ya hori shugabannin gidan rediyon da su tabbatar da dorewar al’adar gidan rediyon ta hada kan kasa da ilimintar da jama’a akan muhimman abubuwan da zasu dabbaka hadin kai da cigaban kasa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: