Yansanda na shirin zanga-zanga domin neman a kara musu albashi da alawus-alawus

0 81

Sufeto Janar na ‘Yansanda, Usman Alkali Baba, yace babu wani dansanda da zai gudanar da zanga-zanga saboda kin aiwatar da karin albashi saboda ya san illar hakan.

Alkali Baba ya sanar da hakan lokacin da yake mayar da martani dangane da rahotannin kafafen yada labarai a jiya dake cewa ‘yansanda na shirin zanga-zanga a ranar 26 ga watan Maris domin neman a kara musu albashi da alawus-alawus.

Ministan harkokin ‘yansanda, Muhammad Dingyadi, a bara yace za a fara aiwatar da sabon tsarin albashin ‘yansanda daga watan Janairun bana, amma hakan bai samu ba har yanzu.

Babban sufeton na ‘yansanda cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya ta hannun mukaddashin kakakin ‘yansanda, Muyiwa Adejobi, yace abu ne mai muhimmanci a jaddada cewa rundunar ‘yansandan Najeriya hukumace mai biyayya ga shugabanni wacce take da dokoki da ka’idojoji wajen bayyana bacin rai kuma babu batun zanga-zanga ko yajin aiki.

Ya bayyana rahoton zanga-zangar da ‘yansanda za su yi da cewa aikin wasu bata gari ne da suka kitsa da nufin bata sunan rundunar da kuma yaudarar jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: