Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya taya murna ga shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, bisa nasarar zabensa domin wa’adin mulki na biyu.

A cikin wani sakon taya murna dauke da sa hannun kakakinsa, Garba Shehu, da aka fitar jiya a Abuja, shugaban kasar yayi nuni da cewa Emmaneul Macron mai shekaru 44, ya kafa tarihin a matsayin shugaban Faransa na farko da ya zarce akan mulki cikin shekaru 20.

Shugaba Buhari ya tabbatar da cewa ingancin mulkin shugaban kasar na Faransa na cigaba da zama abin koyi ga sabbin shugabannin zamani.

Emmanuel Macron ya shafe watanni shida a Najeriya yana aiki a ofishin jakadancin Faransa a shekarar 2002.

Shugaba Buhari yayi nuni da abotar da ta kara karko tsakanin Najeriya da Faransa tun bayan da Emmanuel Macron ya zama shugaban kasa a shekarar 2017.

Yayi nuni da cewa Emmanuel Macron ya ziyarci Najeriya a matsayin shugaban kasa a shekarar 2018 kuma ya cigaba da tabbatar da karfafa alakar tattalin arziki da tsaro da al’adu tsakanin kasashen biyu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: