Labarai

Shugaba Buhari ya umarci Sojoji su ninka kokarin su wajen dakile hare-haren yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasar nan

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya umarci Sojoji su ninka kokarin su wajen dakile hare-haren yan bindiga a yankin arewa maso yammacin kasar nan.

Jihohin Arewa maso yamma na cigaba da fuskantar hare-haren yan bindiga da masu garkuwa da mutane wanda suke lalata dukiyoyi mutane tare da korar su daga gidajen su.

Shugaba Buhari Cikin wata sanarwa da kakakin Malam Garba Shehu, ya rabawa manema labarai, ya umarci sojoji su ninka kokarin su wajen dakile hare haren yan bindigar a Jihar Zamfara.

Shugaba Buhari ya jajantawa iyalan mutanen da hare-haren yan bindigar ya shafa a Jihar ta Zamfara, inda ya ce ya zama dole gwamnatin tarayya da na Jiha su ninka kokarin su wajen dakile kashe-kashe a Jihar.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: