

- Mataimakin Gwamnan jihar Jigawa, Mallam Umar Namadi, shine ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jam’iyyar APC - May 27, 2022
- Shugaba Buhari yace gwamnatinsa tana assasa ginshiki mai inganci na kyakykyawar rayuwa domin yara manyan gobe a Najeriya - May 27, 2022
- Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta haramta bangar siyasa da tare da yin amfani da duk wani makami ga yaran yan siyasa - May 27, 2022
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi alƙawarin taimaka wa ƙasar Sudan ta Kudu a yaƙi da ‘yan bindiga da kuma haɗin kan ƙasar.
Buhari ya bayyana hakan ne a yau Juma’a yayin da yake karɓar baƙuncin wakilin Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.
“Za mu duba halin da kuke ciki don ganin yadda za mu taimaka,” IN JI Buhari cikin wata sanarwa da kakakinsa Fe mi Adesina ya fitar.
Wakilin na musamman, Albino Matham Ayuel, ya yi wa Buhari bayani kan yadda wata ƙungiyar masu ta da ƙayar baya “kamar Boko Haram ɗinku ta aikata kashe-kashe kuma ta wulaƙanci da lalatawa”.
Sanarwar ta ƙara da cea daga baya kuma ya nemi “haɗin gwiwa kan tsaro, musamman ba wa dakaru horo tun da kuna da ƙwarewa kan wannan lamari”.