A halin da ake ciki kuma, mai baiwa shugaban kasa Muhammadu Buhari shawara kan harkokin yada labarai Femi Adesina, ya ce shugaban kasar na da wanda ya fi son ya gaje shi a 2023, amma ba zai ambaci sunansa ba.

Mista Femi Adesina ya bayyana hakan ne a jiya yayin wata tattaunawa da gidan talabijin na Channels.

Ya zuwa yanzu ministan sufuri, Rotimi Amaechi; da na Neja Delta Godswill Akpabio; da na kwadago da ayyukan yi Chris Ngige; da na kimiya da fasaha da kirkire-kirkire, Ogbonnaya Onu, karamin minista a ma’aikatar ilimi, Emeka Nwajiuba sun shiga jerin ‘yan takarar shugaban kasa a karkashin tutar jam’iyyar APC.

Mista Femi Adesina, wanda ya ce shi ba dan jam’iyyar APC bane mai rijista, ya tabo batun yajin aikin ASUU, da kuma yadda shugaban kasa ke da muradin warware matsalar yajin aikin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: