Shugaba Buhari zai kafa sabbin wuraren shakatawa 10 a kasar nan domin dawo da martabar soyayya

0 159

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana kudurin gwamnatinsa na kafa sabbin wuraren shakatawa 10 a kasar nan domin dawo da soyayyar juna a tsakanin yan kasar nan.

Shugaban Buhari ya bayyana hakan ne a wani Bidiyo a wurin taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 wanda ake gudanarwa a birnin New York.

Wannan na kunshe cikin wata sanarwa da Kakakinsa, Mista Femi Adesina, ya sanyawa hannu, kuma aka rabawa manema labarai.

A cewarsa, Shugaba Buhari ya ce yin hadin gwiwa tsakanin gwamnatin da sauran masu ruwa da tsaki, za su taka muhimmiyar rawa wajen dawo da martabar kasar nan, da bunkasa Kasuwanci da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.

Kazalika, Shugaba Buhari ya godewa Shugaban Kasar Costa Rican, Mista Carlos Alvarado Quesada, wanda kasar sa ce ta bada gudunmawa tare da tabbatar da cewa Najeriya ta shiga cikin kawancen da aka kulla domin tabbatar da shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: