Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya zai tafi Belgium a yau Talata don halartar taron haɗin gwiwa tsakanin ƙungiyar haɗin kan Afirka ta African Union (AU) da takwararta ta Tarayyar Turai (EU).

Taron wanda zai gudana a birnin Brussels daga 17 zuwa 18 na Fabarairu, inda shugabannin nahiyoyin biyu za su tattauna matsalolin da ke faruwa a yankunansu.

Wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasa ta ce ana sa ran Buhari zai koma gida ranar Asabar. Ta ƙara da cewa shugaban zai yi amfani da damar wajen tattauna sauran al’amura da wasu ƙasashe.

Abubuwan da shugabannin za su tattauna sun haɗa da batun ilimi da sauyin yanayi da makamashi da zaman lafiya da harkokin mulki da harkokin tattalin arziki.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: