Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan wasu kudirori guda uku da ke da nufin inganta tsarin yaki da safarar kudade da kuma yaki da ta’addanci a Najeriya.

Kudurorin sune Dokar Magance Halasta Kudin Haram ta bana da Dokar Magance Ta’addanci ta bana da kuma Dokar Kwacewa da Kula da Kudaden Sata ta bana.

Shugaba Buhari yayin da yake rattaba hannu kan wadannan dokokin jiya a fadar shugaban kasa dake Abuja, ya ce wadannan kudirorin sun yi daidai da kudurin gwamnatin na yaki da cin hanci da rashawa da halasta kudaden haram, da kuma muhimman batutuwan da suka shafi harkokin mulki da cigaban Najeriya.

Shugaba Buhari ya yabawa majalisun kasarnan bisa juriya da jajircewa wajen ganin Najeriya ta samar da ingantattun dokokin magance matsalar safarar kudaden haram da ta’addanci da kuma samar da karin kudaden shiga.

Ya yabawa majalisun a karkashin Shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da sauran takwarorinsu da suka amince da bukatarsa.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: