Wata Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kano wacce ke zama a Kofar Kudu, ta umurci Majalisar Agajin Lauyoyi ta kasa da ta samar da lauya ga Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sakamakon korar lauyan sa Ambali Muhammad daga shari’ar batanci da ake cigaba da yi masa.

Da kotu ta tambaye shi ko zai gabatar da wani sabon lauya, malamin ya roki a bar shi shi kadai ya ci gaba da shari’ar sa saboda ba zai samu wanda zai tsaya masa ba.

Amma da suke nuna rashin amincewa, tawagar masu shigar da kara karkashin jagorancin Farfesa Nasir Adamu Aliyu ta ce idan aka yi la’akari da girman laifin da ake tuhumarsa da shi, rashin samun lauyan da zai kare shi zai yi mummunan tasiri a shari’ar.

Don haka ya roki kotun da ta bukaci majalisar ba da agajin shari’a ta ba shi lauya kamar yadda sashe na 36 na kundin tsarin mulkin kasarnan ya tanadar.

Mai shari’a Ibrahim Sarki Yola ya amince da rokon sannan ya bukaci majalisar bayar da agajin shari’a da ta samar da lauya ga wanda ake kara.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: