Gwamnatin Tunusiya ta musanta cewa an kama tsohon Firaministan kasar Hamadi Jebali.

Wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook jiya ya ce jami’an tsaro sun tsare tsohon firaministan.

Ita ma jam’iyyar Ennahda mai kishin Islama ta bukaci a sake shi.

Sai dai a yanzu ma’aikatar harkokin cikin gidan kasar ta ce tana binciken wata masana’anta a wani fili mallakin uwargidan tsohon firaminista kuma shine ya dage sai ya raka ta ofishin ‘yan sanda.

Masu suka dai na zargin shugaban Tunisiya Kais Saied da kokarin murkushe ‘yan adawa.

A bara ya rusa majalisar dokokin kasar tare da karbe madafun iko.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: