Gabanin zaben fidda gwani na manyan jam’iyyun siyasa a Najeriya suna sayen daloli lamarin da ke janyo faduwar darajar Naira

0 76

Gabanin zaben fidda gwani na manyan jam’iyyun siyasa guda biyu wato APC da PDP, masu neman tsayawa takara suna sayen daloli a fadin kasar nan, lamarin da ke janyo faduwar darajar naira.

An bayyana cewa dala ta yi tashin gwauron zabi tsakanin naira 550 zuwa 570 a watanni biyun da suka gabata, inda ta tashi zuwa naira 595 a kasuwar bayan fage a jiya.

Bincike ya nuna cewa darajar Naira na ci gaba da faduwa akan dala a kasuwannin bayan fage yayin da jama’a da dama ke neman kudaden kasashen waje da suka fara karanci.

A wani labarin kuma, mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Kano, Zubairu Hamza Massu, ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa jam’iyyar NNPP.

Zubairu Massu ya bayyana ficewarsa daga jam’iyyar APC a wata wasika da ya aikewa shugaban jam’iyyar na mazabar Massu.

Dan majalisar ya kafa hujja da rigingimun da ke faruwa a jam’iyyar da rashin adalci da rashin bin dimokradiyya a matsayin dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: