Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa ya amince da karba-karbar Mulki ga Mutane.

Shugaba Buhari, ya ce Majalisar Kasa ce kadai take da ikon sauya fasalin kasa, karba karba, saboda abune da yake da Alaka da Kundin Tsarin Mulkin Kasa.

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da Kakakinsa Femi Adesina, ya rabawa manema labarai a Abuja.

A cewar Femi Adesina, shugaban ya bayyana hakan ne a lokacin da Jagororin Majalisar Addinai ta Kasa Karkashin Jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmai Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, da Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Kasa CAN, Dr Samson Supo Ayokunle, suka kawo masa ziyara a fadarsa dake Abuja.

Haka kuma ya ce Gwamnatinsa ta jajirce wajen ganin cewa ta samarda kyakkyawan yanayin kasuwanci saboda masu zuba Jari, ta yadda hakan zai samarwa Matasa ayyukan yi, da kuma bunkasa tattalin arzikin Kasa.

Kazalika, Shugaban ya ce Majalisar Zartarwa ta amince da fitar da kudade ga hukumomin tsaro domin kyautata ayyukansu.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: