Labarai

Ana gudanar da aikin shuka bishiyoyi miliyan 5 a kasar Ghana yau Juma’a a wani yunkuri na farfado da martabar dazukan kasar.

Ana gudanar da aikin shuka bishiyoyi miliyan 5 a kasar Ghana yau Juma’a a wani yunkuri na farfado da martabar dazukan kasar.

An bukaci dukan yan kasar su sa hannu a aikin.

Shugaban Kasa Nana Akufo Addo ya ce zai shiga a yi da shi a shirin da za a rika yi duk shekara.

A wani jawabi da ya yi ta bidiyo, ya bukaci ‘yan kasar su killace muhallinsu ta hanyar kula da tsirran da za a shuka.

Hukumomin kasar sun yi kiyasin cewa kashi 80 cikin dari na dazukan kasar Ghana sun lalace saboda lalata muhalli da sare bishiyoyi.

Kasar ta Ghana ta riga ta fara ganin illolin sauyin yanayi.

An yi kiyasin cewa za a samu raguwar kayan abinci da kashi 7 cikin 100 a tsakiyar wannan karnin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: