An raiwato cewa an sace wani jariri dan wata 3 da wasu mata 5 a Anguwar Epe dake bayan makarantar sakandiren gwamnati da Tungan-Maje a babban birnin tarayya Abuja.

Wani mazaunin yankin, wanda yace sunansa Ishaku, yace lamarin ya auku ranar Talata da misalin karfe 10 da mintuna 23 na safe.

Yace wasu daga cikin masu garkuwa da mutanen wadanda suka ja daga a gurare masu muhimmanci a kauyen, sun yi ta harbin iska domin razana makota da jami’an tsaro daga zuwa wajensu.

Ya kara da cewa kafin zuwan yansanda daga ofishin yansanda na Tungan Maje, tuni barayin suka tsere da wadanda suka sata.

An rawaito cewa Tungan Maje, wani kauye mai yawan mutane, daga kan titin Zuba zuwa Gwagwalada, na cigaba da fuskantar hare-hare babu kakkautawa daga yan fashin daji.

Watanni kadan baya aka sace wani tsohon kwamturola na immigration da wasu mutane 5 a yankin.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: